Make your own free website on Tripod.com
WELCOME TO DALHATU ZARAH

Mu Kyakyata

Home
Litattafan Hausa
Tarihin Garin Hadejia
Shafin Musulunci
Ilimin Computer
Wasanni
Sabon Shafi
Tuntube Mu
Labarai
Mu Kyakyata
Addreshin Mu
Hotunan Mu
Hotunan Abokai

Ha!           Ha!!                Ha!!!                 Ha!!!

images.jpg

SHEGU SUN BAYAR DANI
Wani Mahaukaci ya zo ya samu ana sallar gawa, sai ya shiga sahu. Can sai liman yace Allahu - Akbar sai mahukaci ya duka ya kama gwiwa. Ya duba damansa ya ga kowa a tsaye. Ya duba hagu ya ga ba wanda ya duka, sai ya kada kai yace Shegu sun bayar da ni. Ya ci gaba da tafiyarsa.
 
 
DUKA BIYUN
Wani mutum yana kwance ba shi da lafiya, da aka gama abinci sai aka ce Wane wa takila ba zai iya cin tuwo ba, a tambaye shi ko ya fi son a dama masa kunu? Da aka tambaye shi sai ya miko hannunsa yana kada yatsunsa biyu, da kyar yana nishi, ya ce 'Ayi duka biyun'.
 
MAHAUCI DA MATAR SA
Matar Mahauci ta kai shi kara gaban Alkali, aka aika masa sammaci ya zo. Da ya iso sai Alkali, ya sa Dan wanka ya tambayi matar akan me take karar mijinta, sai matar ta ce, 'Ni ba wani abu ya dame ni da shi ba illa rashin wanka.' Aka ce wa Mahauci "to kai kaji. Matarka ta ce ba ka wanka" Mahauci yayi shiru, can sai ya ce 'To gafarta Malam na sawwake mata ta je ta auri kwado, ni kuma na je in nemi akuya.
 
YA KO YI DADI
Wani mutum ya je gidan abokinsa aka kawo musu abinci suna ci. Can sai bakon ya ce, "kai Wane kai kam ka yi sa'a". Ya ce "Wace irin sa'a?, ya ce "Matarka ta iya abinci". Wancan ya yi dariya ya ce "Taka fa?" Sai bakon yace, "Ni tawa me za a yi da irin girkinta. "Sai in hada kayan cefanena mai tsada in kawo mata, sai ta dauka ta kwaba shi ta kwaba, ta kwaba.." yana cikin fadin haka sai yaji motsin takalma. Ya daga kai haka sai ya ga ashe matarsa ce ta leko gidan bai saniba; sai ya ce "ya ko yi dadi".
 
GABA TA KAI NI GOBARAR TITI A JOS
An taba yin wata mace a Jos, wai ita Titi. Wata rana Titi ba ta gida sai gobara ta tashi. Kayan Titi duk suka kone kurmus. Ita kuma mai fuskar jama'a ce, don haka mutane da yawa suka zo mata jaje. Wanda kuma duk ya zo sai ya dan kawo wani abu ya ba ta. Da aka gama jaje sai Titi ta ga abin da ta samu ya zarce wanda gobarar ta cinye mata. Sai ta ce "Ai ni wannan gobarar gaba ta kai ni". Daga nan aka samu in mutum ya rasa wani abu amma rashin ya kawo masa samun abin da ya fi shi, to sai ya ce "Ai ni gaba ta kai ni; gobarar Titi a Jos".

Enter content here

Enter supporting content here

ZARAH BABY